Shugaban NNPC Maikanti Baru ya sanar cewa duk wani dan kasuwa dake siyar da mai fiye da yadda gwamnati ta kayyade zai gamu da hukuncin hukuma
Kamfanin NNPC ta sha alwashi na cewa yan Nijeriya baza su shiga sabon shekara da reshin mai.
Shugaban kamfani NNPC Maikanti Baru ya sanar cewa duk wani dan kasuwa dake siyar da mai fiye da yadda gwamnati ta kayyade zai gamu da hukuncin hukuma.
Ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa ranar juma'a 29 ga watan yau.
Baru ya jaddada cewa tun a a baya ya sanar ma manema labarai cewa akwai wadatacciyar mai wanda zai kai har tsawon sabon shekara amma bisa ga aika-aika wasu yan bata gari aka samu cikas inda suka boye mai domin sanya jama'a cikin masananciyar hali na rashin mai.
Game da lamarin shugaban ya sanar cewa bisa ga yunkurin da shi da jam'an hukuma suka yi na zagayawa gidajen mai domin lura da yanda abubuwa ke gudana, yanzu an fara samun sauki kuma nan bada jimawa ba za'a kawo karshen wahalar.
Daga karshe mai ruwa da tsaki na kamfanin NNPC ya jaddada cewa duk wani dan kasuwa dake boye mai ko kuma ya siyar dashi fiye da kudin da gwamnati ta kayyade (N145) zai gamu da hukuncin doka kana jami'an dake lura da ire-iren haka zasu bada mai ga jama'a kyauta.
Wahalar man fetur: Yan Nijeriya baza su shiga sabon shekara da reshin man fetur – inji NNPC
CLICK HERE TO READ FULL CONTENT
Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING