Featured post

Sean Dampte UK based singer, drops new track,‘Energy’

Friday, 23 February 2018

Hoton tuna baya: Ko kuna iya gane ko wacece wannan?

tsohon hoton mawakiyar Nijeriya lokacin kuruciyar ta

Tana daya daga cikin mawakan nijeriya daga arewacin kasar

Shaharrariya mawakiyar nijeriya kuma daya daga cikin gwarzaye a wannan fannin da arewa ke alfahari da ita Hadiza Salma Blell wanda aka fi sani da Di'ja ta tuna baya da wanna tsohon hoton ta.

Di'ja ta wallafa hoton lokacin kuruciyar ta a shafin ta na Instagram.

 

Mawakiyar wanda yar ruwa biyi ce kasancewa mahaifin ta dan kasar Sierria Leone ne kuma mahaifiyar ta yar Zaria ce nan kasar Nijeriya tayi fice a kasar da salon wakar da take mai nishadantarwa bisa zakin muryar ta.

Tayi zama a kasar Nijeriya da Sierra leone da Amurka da Canada kuma mahaifin ta tsohon mataimakin minista ne a kasar Sierra leone dake yankin yammacin Afirka.

Di'ja ta fara harkar waka gadangadan a cikin 2008 kuma ta samu karramawa tare da amsar lambar yabo na beat music Awards a 2008.

A cikin 2012 sannane mawaki kuma shugaban kamfanin Mavin records Don jazzy ya kaddamar da ita cikin inuwar mawakan kamfanin shi.

Di'ja tayi aure a shekarun baya wanda aka yi cikin sirri ba tare da sanin jama'a kuma Allah ya albarkace auren da samun da namiji.

Hoton tuna baya: Ko kuna iya gane ko wacece wannan?



CLICK HERE TO READ FULL CONTENT

Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING