Featured post

Sean Dampte UK based singer, drops new track,‘Energy’

Tuesday, 13 March 2018

Abdulmumin Jubrin: Bayan watanni da dakatarwa majalisar wakilai ta dawo da Abdulmumin Jubrin

My suspension is a learning curve - Abdulmumin Jibrin says

Ya zargi kakakin majalisar da wasu masu hanu-da-shuni na zauren da yi ma kasafin kudin kasa gyaran fuska

Majalisar wakilai ta dawo da dan majalisar Abdulmumin Jubrin bayan dakatar dashi na tsawon kwana 180.

Dan majalisar mai wakiltar jihar Kano ya samun hukuncin bayan rahoton da kwamitin ladabtarwa na majalisar ta bayyana ma zauren bisa zargin da yayi.

Ya zargi kakakin majalisar da wasu masu hanu-da-shuni na zauren da yi ma kasafin kudin kasa gyaran fuska.

Kwamitin tayi bincike kan tabbacin faruwar hakan kana ta umarce shi da rubuta wasikar neman gafara.

A zaman da yan majalisar suka yi yau talata 13 ga wata maris 2018 kakakin majalisar Yakubu Dogara ya sanar ma sauran yan majalisar cewa shi Abdulmumin ya tura wasikar neman gafara ga zauren.

kakakin yace Jubrin ya cika ka'idoji da aka kafa masa tare da rubuta wasikar neman gafara, don haka yana iya dawowa aiki duk lokacin da ya shirya.

Abdulmumin Jubrin: Bayan watanni da dakatarwa majalisar wakilai ta dawo da Abdulmumin Jubrin



CLICK HERE TO READ FULL CONTENT

Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING