Featured post

Sean Dampte UK based singer, drops new track,‘Energy’

Monday 2 April 2018

Fadar shugaban kasa: Jerin sunayen wadanda suka saci kudin kasa

Ministan labarai da al'ada Lai Muhammed

Sai dai jam'iyar PDP ta kalubalanci wannan sunayen inda take cewa babu daya daga cikin dukkan mutanen da aka fitar da sunayensu da kotu ta samu da laifi

Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen jami'an jam'iyar PDP da ta gwamnatin data shude wadanda suka yi wa arzikin Nijeriya cin zomo ga harawa tare da yawan kudaden da kowannensu ya sata.

Bayan jam'iyar adawa ta PDP ta bukaci a fitar da sunayen wadanda gwamnatin jam'iyar APC mai ci take zargi da laifin wawure kudin jama'a, ministan watasa labarai Lai Muhammed ya fitar da jerin sunayen.

Ga jerin sunayen kamar haka;

1. Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus: Ya karbi miliyan 200 ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA).

2. Tsohon sakataren kudin jam'iyyar PDP: A ranar 24 ga watan Oktoba, 2014, ya karbi miliyan N600m daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a kan harkar tsaro.

3. Tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Olisah Metuh: Ana tuhumar sa da karbar biliyan N1.4bn daga ofishin tsohon NSA.

4. Dakta Raymond Dokpesi: Shugaban kamfanin DAAR; mai gidan talabijin na AIT da gidan Radiyon Ray Power. Ana tuhumar sa da karbar biliyan 2.1 daga ofishin tsohon NSA.

5. Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara, Dudafa Waripamo-Owei: An gurfanar da shi bisa boye kudi miliyan N830m a asusu daban-daban.

6. Dan uwan tsohon shugaban kasa, Robert Azibaola: An gurfanar da shi gaban kotu ranar Alhamis bisa tuhumar karbar Dala biliyan $40m.

Ministan ya kuma fitar da sauran sunayen wasu da ake ma zargin kawo ma tattalin arzikin kasa cikas inda yace ba su shi ya kirkira sunayen ba domin mafi yawancin su suna gaban kotu inda ake tuhumar su kan laifin da suka aikata kuma wasu daga cikin su suna son kotu ta basu dama su mayar da wani kaso na daga cikin kudaden da suka sata domin kotu ta sake su.

A karo na biyu na jerin sunayen wadanda ake zargi da kuma adadin kudin da suka sata akwai:

1. Tsohon NSA Sambo Dasuki: $2.1bn, N126 billion, $1.5 billion, Fam 5.5 miliyan

2. Tsohon ministan man fetur Diezani Alison-Madueke: N23bn, $3 billion

3. Laftanal Janar Kenneth Minimah: N13.9 billion

4. Laftana Janar Azubuike Iejirika: N4.5 billion

5. Tsohon shugaban soji, Alex Barde: N8billion

6. Tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde: N40 billion

7. Air Marshal Adesola Amosun: N21.4 billion

8. Tsohon ministan FCT, Sanata Bala Abdulkadir: N5 billion

9. Sanata Stella Oduah: N9.8 billion

10. Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu: N1.6 billion

11. Tsohon gwamnan jihar Flato, Jonah Jang: N12.5 billion

12. Tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda: N1.5 billion, $829,800

13. Sanata Peter Nwaboshi: N1.5billion

14. Aliyu Usman: N512 million

15. Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja: N500 million

16. Tomi Ikimi: N300 million

17. Femi Fani-Kayode: N866 million

18. Hassan Tukur: $1.7 million

19. Nenadi Usman N1.5 billion

20. Benedicta Iroha: 1.7 Billion

21. Aliyu Usman Jawaz: N882 million

Sai dai jam'iyar PDP ta kalubalanci wannan sunayen inda take cewa babu daya daga cikin dukkan mutanen da aka fitar da sunayensu da kotu ta samu da laifi.

A wata sanarwa jam'iyar adawa tayi a shafin ta na twitter tana mai cewa, "jerin sunayen da ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammed ya wallafa na nuna cewa APC da shugaban Najeriya ba su da wata hujja da ke nuna PDP na da laifi."

PDP tace gwamnati ta fitar da sunayen ya'yan ta ne domin bata masu suna.

Fadar shugaban kasa: Jerin sunayen wadanda suka saci kudin kasa



CLICK HERE TO READ FULL CONTENT

Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING