Featured post

Sean Dampte UK based singer, drops new track,‘Energy’

Monday 3 September 2018

AMVCA 2018: Fim wanda Ali Nuhu bai taba irin ta ba ta lashe kyauta a bikin bana

AMVCA 2018

Shirin Mansoor wanda jarumin ya shirya tayi zarra wajen zama shiri mafi kayatarwa a rukunin wasan gargajiya na harshen hausa.

Fitaccen jarumin fina-finan hausa ta dandalin kannywood Ali Nuhu ya lashe kyautar AMVCA sakamakon shirin fim da ya shirya mai suna MANSOOR.

Gasar African Magic Viewers Choice Awards wanda aka shirya a birnin Legas ranar asabar 1 ga watan Satumba, shirin MANSOOR ya lashe kyautar shiri mafi kayatarwa.

Shirin ta lashe kyautar sabanin sauran fina-finai da aka hada su takarar na daga cikin fitattun shirye-shirye na rukunin hausa.

A jawabin sa yayin da ya amshi kyautar Ali Nuhu ya mika godiyan sa jaruman mda ma'aikatan da suka taka rawar ganinĂ‚  wajen shirya shirin MANSOOR.

Ă‚ 

Hirar shi da wakilin BBC hausa jarumin yace "Ina ganin Mansoor ya samu wannan nasara ce saboda bamu taba shirya fim wanda aka yi amfani da fasahar kirkire-kirkire kamar sa ba; mun kashe kudi sosai sannan mun yi amfani da na'urori na zamani wurin daukar fim din."

Shirin wanda ke isar da darasi akan yadda mutum zai gudanar da rayuwar sa ba tare da tsangwama ba domin bai san irin jarabtar da Allah ya shirya masa.

Sabbin fuskoki Maryma Yahaya da Umar M.Shereef suka fito a matsayin jaruman shirin.

AMVCA 2018: Fim wanda Ali Nuhu bai taba irin ta ba ta lashe kyauta a bikin bana



CLICK HERE TO READ FULL CONTENT

Brought to you by: RIDBAY | WEBSITE DESIGN & DIGITAL MARKETING